Matasa da basu gaza 80 ba da suka shiga cikin Jeji ɗebo Itatuwan girki sun shiga hannun 'yan ta'adda da ake zaton sun yi garkuwa da su a jihar Zamfara. Legit ya wallafa.
Vanguard ta rahoto cewa lamarin, wanda ya auku a ƙauyen Wanzamai da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Jumu'an nan ya jefa mutanen ƙauyen cikin firgici da tashin hankali.
Duk wani yunkurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ko gwamnatin Zamfara ya ci tura har zuwa yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton.
Amma iyayen da aka yi garkuwa da 'ya'yansu sun shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa yan ta'addan sun sace matasan yaransu maza da mata yayin da suka je ɗebo Itace a Jeji.
Ƙarin bayani na nan tafe...
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI