Wata matashiya mai shekara 26, Rukayat Motunrayo Shittu, ta zama zababbiyar 'yar Majalisar Dokokin Jihar Kwara. Rahotun Jaridar Aminiya.
Zababbiyar 'yar matashiyar ta kasance 'yar jarida, kafin ta tsunduma harkar siyasa.
Rukayat ta Jam'iyyar APC ta yi nasara ne bayan ta lallasa abokin karawarta, Abdullah Magaji, na jam'iyyar PDP.
Baturen zaben, Farfesa Akeem Olasunkanmi Ijaiya, ya sanar cewa Rukayat Motunrayo Shittu, ta yi nasara ne bayan da ta samu kuri'u 7,521, shi kuma Abdullah Magaji na PDP ya samu 6,957.
A halin yanzu Rukayat, za ta kasance mafi karancin shekaru a cikin 'yan majalisar dokokin jihar.
BY ISYAKU.COM