Yan Sandan Katsina Sunyi Artabu Da Yan Ta'adda, An Sheke Daya, An Kwato AK-47


Jami'an yan sandan Jihar Katsina sun yi musayar wuta da yan bindiga ranar Litinin a titin Danmusa/Yantumaki a da ke karamar hukumar Danmusa har sun kashe dan ta'adda daya. Legit ya wallafa.

Yan sandan sun ce sun kwato bindiga kirar AK-47 lokacin bata kashin, rahoton jaridar The Punch.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ranar Talata, ya ce yan bindigar sun tare titin a daidai kauyen Kesassa.

Isah ya ce:

''Ranar 27 ga watan Maris, 2023, da misalin 2:30 na rana, mun samu kiran gaggawa cewa gungun yan ta'adda, su na harbi kan mai uwa da wabi da bindigun AK-47, sun tare titin Danmusa-Yantumaki, da ke karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
''Nan take, shugaban ofishin yan sanda na Danmusa, ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa yankin, su ka datsi yan ta'addar tare yin nasarar kawar da su.
''A binciken da aka gudanar a wajen, an tsinci gawar dan bindiga daya da aka harbe. Sannan, an samu bindiga kirar AK-47 da jakar harsashi dauke da harsashi 22 ma su rai a wajen.''
Isah ya ce su na hasashen an kashe yan ta'adda da yawa ko kuma sun gudu da munanan raunin bindiga.

''Ana ci gaba da bincike a dajika mafi kusa da nufin kama su a raye ko a mace,'' in ji shi
Isah ya kuma roki mutanen yankin, da su sanar da yan sanda idan sun hangi wani da irin raunin da su ke zargi.

Ya kara da cewa:

''Rundunar yan sanda ta yaba da kokarin da yan sandan su ka nuna, na kakkabe yan ta'adda cikin salo da kwarewa.''

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN