Ta faru: An yi wa Alkalin Kotun Majistare korar kare daga aiki, an rage wa wasu alkalai 2 mukami a jihar arewa


Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Neja ta kori alkalin kotun majistare da ke karamar hukumar Magama Mohammed Bako Iya tare da sauke wasu alkalan kotun shari’a guda biyu Abdullahi Nasiru da Mohammed Baba Enagi.

 An kori Iya ne saboda rashin da’a da kuma amfani da matsayinsa na Alkalin Kotun Majistare ba bisa kaida ba.

Yayin da sauran alkalan kotunan Shari’a da ke Minna da Badeggi, aka sauke su bisa rashin da’a da cin zarafin mukamai, sannan kuma za su yi aikin koyarwa na shekara daya a wasu kotuna.

 Wasu daga cikin zarge-zargen da ake wa korarren Alkalin sun hada da yin amfani da matsayinsa na Alkalin Kotun Majistare ya kare wani Saba Idris wanda jami’an ‘yan sanda ke nema.

Da kuma yin amfani da karfin ofishinsa wajen tsoratarwa da karbar Naira 400,000 daga hannun makiyayan da shanunsu suka lalata masa gonar wake.  

An gano cewa Mohammed Bako shi ne Alkali a shari’ar sa kuma ya yi amfani da matsayin ofishinsa wajen daukar wa kansa fansa.

 Sakataren hukumar, Abdulrahman Ahmed Garafini ya ce an dauki matakin ne biyo bayan shawarar kwamitin da aka kafa domin binciken koke-koken da ake yi wa alkalan.

 An yanke hukuncin korar daga aiki da rage wa alkalan mukqmi ne a taro na 136 a ranar 21 ga Maris, 21. Garafini ya ce;

 “Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Neja ta samu kararraki guda bakwai, inda uku daga cikinsu sun danganci alkalin Kotun Majistare da aka kora, biyu daga cikin ukun kuma wadanda suka shigar da karar sun tabbatar da isassun hujjoji a kan korafinsu”.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN