An harbe mutum daya har lahira a birnin Kisumu da ke yammacin kasar Kenya yayin da masu zanga-zanga suka fito domin nuna adawa da tsadar rayuwa. BBC ya ruwaito.
An kuma yi arangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a wasu matsugunan da ba na yau da kullun ba a birnin Nairobi.
Gwamnati dai ta tura jami'an tsaro domin dakile zanga-zangar da madugun 'yan adawa Raila Odinga ya kira, amma hakan ya kara ruruta wutar rikici.
Ma'aikatar harkokin cikin gida da kuma sufeto janar na 'yan sanda sun bayyana zanga-zangar a matsayin haramtacciya.
A halin yanzu dai shugaba William Ruto yana wata ziyarar aiki a kasashen Belgium da Jamus.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI