Shugabannin siyasa na soji da na farar hula a Sudan sun fara tattaunawa a birnin Khartoum kan mayar da mayakan da ke samun goyon bayan gwamnati RSF karkashin rundunar soji.
Wannan, da sanya sojoji a karkashin ikon farar hula, sune muhimman bukatun kungiyoyin farar hula wadanda suka taimaka wajen hambarar da shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019. BBC ta ruwaito.
Tattaunawar ta ranar Lahadi wani bangare ne na yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a cikin watan Disamba, da nufin share fagen komawa kan tafarkin dimokuradiyya, wanda kuma ya kamata a amince da shi a hukumance cikin kasa da makonni biyu.
Babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki shekaru biyu da suka gabata ya ce yana son kawo karshen sojojin da ke goyon bayan gwamnatocin kama-karya a Sudan.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI