Ebonyi - The Punch ta rahoto cewa a daren ranar Alhamis ne wasu yan bindiga suka tare tawagar motoccin dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance a jihar Ebonyi, Bernard Odo.
Hadiminsa na bangaren watsa labarai, Charles Otu, ya tabbatar da harin, yana mai cewa dan takarar yana hanyarsa na dawowa ne daga kamfen a lokacin da yan bindigan suka tare shi a Rest House kan babban hanyar Enugu/Abakaliki.
An tattaro cewa yan bindigan sun bude wa tawagar wuta kuma sun harbi direban mota kirar Sienna da ke dauke da Odo.