Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun bude wa ayarin motoccin dan takarar Gwamna wuta, sun bindige direbansa


Ebonyi - The Punch ta rahoto cewa a daren ranar Alhamis ne wasu yan bindiga suka tare tawagar motoccin dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance a jihar Ebonyi, Bernard Odo.


Hadiminsa na bangaren watsa labarai, Charles Otu, ya tabbatar da harin, yana mai cewa dan takarar yana hanyarsa na dawowa ne daga kamfen a lokacin da yan bindigan suka tare shi a Rest House kan babban hanyar Enugu/Abakaliki.


An tattaro cewa yan bindigan sun bude wa tawagar wuta kuma sun harbi direban mota kirar Sienna da ke dauke da Odo. 

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN