Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarci a cafke duk wanda ba ya karɓan tsohon takardun N200, N500, N1000 a jihar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya ce tsoffin takardun naira guda uku da aka sauya suna da halascin amfani har zuwa lokacin da Kotun Koli zata yanke hukuncin ƙarshe kan Kes ɗin da jihohi uku suka kai FG da CBN.
Matawalle ya bayyana haka ne a wurin bikin rantsar da manyan alƙalai da sabbin naɗe-naɗen hadimai wanda ya gudana a gidan gwamnatinsa, Chamber II a Gusau.