Type Here to Get Search Results !

‘Yan sanda sun tabbatar da kashe 'yan sa kai 41 da ‘yan ta’adda suka yi a jihar Katsina

 


Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar ‘yan kungiyar ‘yan banga 41 da aka fi sani da ‘Yansakai’ a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai a dajin Yargoje. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah ya raba wa manema labarai ranar Juma’a a Katsina. “A ranar Laraba, 1 ga Fabrairu, 2023 da misalin karfe 22:00, ‘yan ta’addan da yawansu dauke da bindigar AK 47, suka kai hari gidan wani Alhaji Muntari da ke Unguwar Audu Gare, Kandarawa, karamar hukumar Bakori, suka kuma yi awon gaba da shanu 50.  da tumaki 30. “Daga baya, a ranar 2 ga Fabrairu, da misalin karfe 10:00, kungiyoyin Yansakai daga kauyuka 11 na karamar hukumar Bakori suka sake haduwa suka bi ‘yan ta’addan da nufin kwato dabbobi da yan ta'addan suka kora. “Sun bi hanyar ‘yan ta’addan zuwa wani wuri a dajin Yargoje, abin takaici, ‘yan ta’addan sun shirya tare da kai harin kwantan bauna kan Yan sakai. "Yan bindigar sun harbe Yansakai 41 tare da raunata wasu biyu," in ji shi. Isah ya ce, Kwamandan yankin na Malumfashi, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kwashe gawarwakin da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kankara. Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da aikin hadin gwiwa na jami’an tsaro domin kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies