Delta - Wani kwastoman banki ya yanke jiki ya fadi matacce cikin harabar wani banki bayan kwashe awanni kan layi a garin Agbor na jihar Delta. Legit.ng yawallafa.
Wannan abu ya auku ne ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023 a karamar hukumar Ika ta kudu, rahoton Tribune.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwan wannan lamari.
DSP Bright Edafe ya ce mutumin ya shiga bankin karban katin ATM dinsa ne.
A cewarsa:
"Labarin dake yawo cewa wani mutumi ya yanke jiki ya fadi matacce yayin kokarin cire kudi ba an yi karin gishiri cikin miya. Ya yanke jiki ya fadi ne yayin layin karban sabon katin ATM."