‘Yan sanda sun kama wata mata mai safarar makamai ga ‘yar bindiga a Zamfara



Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mata da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai da alburusai.

 Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa rundunar ta kuma kwato harsasan bindigar AK 47 guda 325 daga hannunta.

 Haka kuma ta yi nasarar damke wasu mutane da ake zargi da mallakar fakitin MTN Sim guda 1000 masu rajista.

 Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Gusau.

 Shehu ya ce an kama wadda ake zargin ‘yar bindigar mai suna Fatima Sani mai shekaru 35 ne biyo bayan rahoton sirri da aka samu kan zarginta da bayar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihar daga garin Lafia a jihar Nasarawa.

 Ya ce: ''A ranar 13 ga Fabrairu, 'yan sanda masu bincike sun kama wanda ake zargin 'yar bindigar ce dauke da harsashi 325.

 “Kamen ya biyo bayan bayanan sirrin da aka samu game da tafiyar ta daga garin Lafia a jihar Nassarawa zuwa ga wani kasurgumin dan bindiga da ke aiki a dajin Zamfara.

 “A yayin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta shiga harkar.

 “Ta kuma sanar da mu cewa tun da farko ta bayar da bindigu kirar AK 47 guda uku da harsashi 1000 na AK 47 ga ‘yan bindiga da ke aiki a jihar.”

 PPRO ta kara da cewa matar wadda ‘yar asalin garin Kaura-Namoda ce a jihar Zamfara nan ba da jimawa ba za a gurfanar da ita a gaban kotu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN