Type Here to Get Search Results !

Tashin hankali: Wata mata mai tabin hankali ta jefa jaririya a masai


Jami’an hukumar kashe gobara a jihar sun ceto wata jaririya da mahaifiyarsa mai tabin hankali ta jefa a masai.

An ceto jaririyar a raye jim kadan bayan da mahaifiyar mai suna Hauwa Muhammad ta jefa ta a masai, Punch ta ruwaito.

Legit ta wallafa cewa da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya ce:

“A ranar Laraba, 15 ga watan Faburairu, 2023, hukumar kashe gobara ta jiha ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:49 na safe, daga daya daga ma’aikatanmu, Ibrahim Umar Muhammad da ya sanar da faruwar lamarin a Sabon Titi Gidan Kankara a Kano ta Tsakiya.

Ma’aikan kwana-kwana sun gaggauta zuwa wurin da misalin karfe 10:54 na safe inda suka tarar da mata mai shekaru 25 mai suna Hauwa Muhammad, wacce aka ce tana da tabin hankali ta jefa diyarta a masai.

“Saboda haka, ‘yan kwana-kwana da suka iso wurin sun shiga aikinsu, sun kuma yi nasarar ceto jaririyar a raye tare da mika ta ga kakanta, Abubakar Umar Usman da ke unguwar Sabon Titi.”
Abdullahi ya kara da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin kafin sanar da al’umma cikakken bayanin yadda abin ya faru, Pulse ta tattaro.

Hukumomin tsaro a Najeriya sun sha ceto irin wadannan yaran daga hallaka bayan samun tsaiko daga iyayensu masu tabin hankali.

A wani labarin kuma, wata budurwa ‘yan yankin Kudancin Najeriya ta yi tattaki zuwa jihar Kano domin ganin saurayinta da ya zauce, ta dauke shi zuwa garinsu.

A bidiyon da ta yada, ta bayyana yadda take nemansa da kuma yadda ta yi nasarar samunsa a Kano kana ta tabbatar da daukarsa zuwa asalin garinsu domin neman magani.

A cewar budurwar, saurayin nata ya kasance jami’in soja, amma wasu mutane suka yi masa tsafi ya haukace babu gaira babu dalili.

BY ISYAKU.COM

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies