Don haka ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da ikon da sassan da suka dace na kundin tsarin mulkin Najeriya suka ba su na tsige shugaba Buhari saboda yunwa da wahala da aka jefa ‘yan Najeriya da sunan tsara tattalin arziki ta hanyar yin musanya da sabbin takardun kudi na Naira.
Bishop Udeh wanda kuma shi ne babban mai kula da Mount Zion Faith Global Liberation Ministries (aka "By Fire By Fire"), Nnewi, jihar Anambra, ya ce ya kamata a kori Gwamnan Babban Bankin CBN, Godwin Emefiele daga ofis sannan kuma a gurfanar da shi gaban kotu. domin cin mutuncin yan Najeriya.
Ya ce abin takaici ne yadda ’yan Najeriya ke yawo a kan tituna suna neman sabbin takardun Naira ba tare da samun biyan bukata ba, kuma su Buhari da Emefiele sun shagaltu da gaya musu cewa su yi hakuri su jira su sabbin takardun Naira a lokacin da talakawa ke mutuwa saboda yunwa.
Ya ce abin da ya fi daure kai shi ne yadda gwamnatin tarayya ta ki bin umurnin kotun koli na ba da damar tsohon takardun naira su zauna tare da sabbin takardun har zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu a lokacin da ake sa ran kotun koli za ta yanke hukunci na karshe kan karar da wasu Gwamnonin jihohi suka shigar suna adawa da gwamnatin tarayya dangane da batun sabon kudin Naira.