Ta faru: An kamashi da kokon kan mutum guda 3 a jihar arewa makonni kafin zabe (Hotuna)

 


Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wani mutu.m mai suna Abdulrahman Woru mai shekaru 38 da haihuwa, bisa laifin mallakar kokon kan mutum a Babana, karamar hukumar Borgu ta jihar a ranar 24 ga watan Janairu. Daga shafin isyaku.com


 A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya fitar, ya ce wanda ake zargin yana zaune a Babana, dan kauyen Gbesewona ne na Jamhuriyar Benin.


 A cewar Abiodun;


 A lokacin da aka gudanar da bincike a gidansa, an gano wani kokon kan mutum, guda uku da ake zargin hakarkarin mutane, gumaka biyu da kuma tsabar kudi CFA 5000 na kudin Jamhuriyar Benin.  Yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa kokon kan mutumin da aka gano nasa ne.  Ya yi ikirarin cewa ya yi hijira ne daga jamhuriyar Benin zuwa Najeriya kimanin shekaru hudu da suka gabata don yin sana’ar sa, ba tare da takardar shige da fice ba, kuma shi likitan gargajiya ne.



 Abiodun ya kuma ce wanda ake zargin ya kara da cewa ya yi tattaki zuwa jamhuriyar Benin kwanan nan, kuma a lokacin da ya shiga Najeriya ya ga wata jaka a hanya da kokon kai a cikinta.


 Ya ce (wanda ake zargin) ya daure shi a kan babur dinsa ya kai shi gida, domin ya yi imanin cewa zai yi amfani ga aikinsa, kuma bai kai rahoto ga ‘yan sanda ba.  Rundunar ta yaba da irin goyon bayan da ‘yan Neja da sauran jama’a suke ba su, sannan ta bukaci da kada su yi kasa a gwiwa wajen sanar da ‘yan sanda idan suka ga wani bakon abu a cikin muhallinsu domin su shiga cikin gaggawa.


 Abiodun ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata kotun da ke da hurumin gurfanar da shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN