Ɗan TikTok ɗin nan Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya ya musanta cewa su ne suka yi ƙarar Murja a gaban Kotu. Rahotun Dala FM.
Dala FM ta ruwaito cewa a zaman Kotun sharia'ar Musulunci ta Filin Hoki da ke Kano mai gabatar da ƙara ya gabarta da tuhume-tuhume ga Murjan wanda ya bayyana cewa Idris da Aisha Najamu ta Izzar So ne suka yi ƙarar ta.
Sai dai a hirarsa da Dala FM a yau Jumu'a Idris ya musanta inda ya ce su basu kai Murja ƙara ba.
Dala FM ta tuntubi kakakin Kotunan Musulunci na Kano a kai, wanda ya bayyana cewar abin da aka gabatar a Kotu shi ne abin da suka samu daga wajen Æ´an sanda.
Mun so ji daga bakin rundunar Æ´an sandan Kano amma har kawo lokacin haÉ—a wannan rahoto ba su ce komai ba.
Ga bayanin da Ashir Idris ya yiwa Dala FM Kano.
Rubuta ra ayin ka