Emefiele Karya ya shararawa shugaba Buhari: Mai magana da yawun shugaban kasa

 


Abuja - Babban hadimin shugaban kasa kan lamuran jama'a, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa karyar kawai gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya shararawa shugaba Muhammadu Buhari. Legit.ng ya wallafa.


Ngelale yace maganar cewa akwai isassun kudi a cikin gari babu kamshin gaskiya ciki,


Ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar a tashar TVC inda yace mutane su daina ganin laifin shugaba Buhari, bayanan da ya samu yake amfani da su.


Ya ce mutane bai zai taba yin abu don tsanantawa jama'a da gayya ba.


A cewarsa:


"Abinda muke yi shine tabbatar da cewa shugaban kasa na samun labaran gaskiya kuma labarin da CBN ya bada cewa an baiwa bankuna isassun kudi a fadin tarayya karyar banza ne. Wannan ya bayyana yanzu."

"Shugaban kasa na jama'a ne, labaran karya kawai yake samu daga wajen CBN, shi yasa aka kara wa'adin daga Junairu 31 zuwa 10 ga Febrairu."

Shugaba Buhari Yace 'Yan Najeriya su Bashi Kwana 7 don Magance Matsalar Sabbin Kudi

Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF sun yi tawaga ta musamman zuwa wajen shugaba Muhammadu Buhari game da lamarin karancin takardun Naira a fadin tarayya.


Yan Najeriya na wahala kan rashin isassun takardun Naira bayan tilastasu mayar da tsaffin kudadensu bankuna.


Gwamnonin sun kaiwa shugaba Muhammadu Buhari kokensu inda suka bukaci ya soke lamarin daina da amfani da tsaffin takardun Naira gaba daya.


Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa babu inda aka taba irin wannan a fadin duniya; inda za'a ce cikin yan kwanaki a kwashe dukkan tsaffin kudade daga hannun jama'a.


Bayan jin kokensu, shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci su bashi kwanaki bakwai kacal don ya magance wannan matsala.


Yan Najeriya har sun fara kwana a gindin na'urorin ATM kawai su samu cire kudadensu na halaliya da suka kai banki da kansu yan kwanaki kadan da suka gabata.

2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Allah ya kyauta

    ReplyDelete
  2. Ana Abu da ganga, ace baisani BA, to ai Shi Allah Ya kuma bar duk mai hannu aciki da Shi.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN