Yanzu Yanzu: Tinubu ya shiga sabon matsala yayin da PDP ta saki jerin Gwamnoni da Sanatocin APC da ke yi wa Atiku aiki


Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa akalla gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 11 ne suke yiwa dan takararsa na shugaban kasa, Atiku Abubakar aiki. Legit.ng ya wallafa.

Daniel Bwala, kakakin kwamitin ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Independent a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu.

Bwala ya kuma bayyana cewa, zuwa Disambar 2022, sanatoci 37 da yan majalisar wakilai 15 a APC suna aiki don ganin Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Jawabinsa na cewa:

"A farkon makon Disamba, muna da gwamnonin APC 11 da suke goyon bayanmu kuma har yanzu akwai wasu a hanya. Muna da sanatocin APC 37 da yan majalisar wakilai 15. Wannan a makon farko na Disamba ne fa. Zuwa yanzu guda nawa kuke ganin mun sake samu."

Bwala ya fadi hakan ne yayin da yake martani ga ikirarin Kassim Afegbua, jigon APC da ya ce kimanin gwamnonin jam'iyyar 3 na yiwa Atiku Abubakar na APC aiki

Afegbua, tsohon kwamishinan labarai na jihar Edo ya yi zargin cewa yana da bayanan sirri cewa Atiku ya yi ganawar sirri da gwamnonin a Dubai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN