2023: Atiku zai sake bude iyakokin Najeriya - Tambuwal


Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto a ranar Asabar din da ta gabata ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai sake bude iyakokin kasar nan, idan har aka zabe shi a zaben 2023 mai zuwa. Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito

Tambuwal, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ne ya bayyana haka a taron yakin neman zaben jam’iyyar PDP a karamar hukumar Illela.

A cewarsa, dan takarar shugaban kasa na PDP yana da kyawawan tsare-tsare ga kasar.

"Wadannan sun hada da sake bude iyakokin kasar, magance kalubalen rashin tsaro da samar da ababen more rayuwa ga 'yan Najeriya," in ji shi.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa a jihar tana tausayawa al'ummar Illela na daya daga cikin yankunan da hare-haren 'yan fashi ya fi shafa.

"Duk da haka, duk da kalubalen rashin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kuma mummunan tasirin COVID-19, mun aiwatar da ayyuka da yawa a karkashin kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha da ayyukan zamantakewa, da sauransu," in ji shi.

A nasa jawabin, DG, Sokoto Campaign Management Council, Alhaji Yusuf Sulaiman, ya bukaci al’ummar yankin da su zabi ci gaba da gudanar da mulki ta hanyar jefa kuri’a ga jam’iyyar PDP.

Malam Sa’idu Umar, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP ya yi alkawarin cewa aikin kasuwar duniya a Illela wpld  ya samu kulawar da ya kamata daga gwamnatinsa, idan aka zabe shi.

Shi ma a karamar hukumar Kware, Umar ya ce yana da kulawa ta musamman ga al’ummar jihar baki daya.

Ya yi alkawarin dorewar abubuwan da Tambuwal ta gada tare da kaddamar da wasu ayyukan raya kasa, idan aka zabe shi.

A nasa bangaren, Alhaji Mannir Dan’iya, dan takarar kujerar Sanatan Sakkwato ta Arewa a karkashin jam’iyyar PDP kuma mataimakin gwamna mai ci ya shaida irin nasarorin da gwamnati mai ci ta samu a jihar.

Ya bukaci al’ummar jihar da su mayar da martani ta hanyar jefa kuri’a ga jam’iyyar PDP, ya kara da cewa an shirya ayyukan raya kasa da dama a karamar hukumar Kware a cikin kasafin kudin 2023. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN