Wasu ‘yan daba sun kai wa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto hari a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu. Legit.ng ta wallafa.
Vanguard ta ruwaito cewa Tambuwal da wasu 'yan majalisar sa na dawowa daga yakin neman zaben jam'iyyar PDP a kananan hukumomin Silame da Wamakko na jihar lokacin da aka kai musu hari.
A cewar wata majiya, 'yan daban sun jefi ayarin motocin gwamnan tare da lalata gilashin mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a SUV.
Haka kuma an huda bangon bayan motar babban sakataren gwamnan ta SUV.
Tambuwal da mataimakinsa, Manir Muhammad ba su ji rauni ba a harin. Sauran jiga-jigan da ke cikin ayarin sun hada da dan takarar gwamna na PDP da abokin takarar sa, Saidu Umar da Sagiru Bafarawa.