Wasu ‘yan bindiga sun sace Kanar mai ritaya da yara biyu a Zamfara


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kanar Rabi’u Yandoto mai ritaya da ‘ya’yansa biyu a hanyar Gusau zuwa Tsafe a jihar Zamfara.

Wani shaidan gani da ido Mohammed Hassan ya shaida wa jaridar Punch cewa Yandoto za su je garinsu ne tare da ‘ya’yansa guda biyu a daren Lahadi inda ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna aka kai su daji.

Hassan ya ce;

“’Yan bindigar sun yi wa kanar mai ritaya kwanton bauna ne a daren ranar Lahadi inda suka yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa biyu da wasu biyu da aka kashe.

"Mun ji karar harbe-harbe kuma muka fara gudu zuwa cikin daji saboda tsoron 'yan bindigar amma daga baya muka gane cewa Kanar Yandoto ne harinsu."

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Yandoto wanda shine shugaban kungiyar siyasar Zamfara ta All Progressive Congress mai suna ‘Wake da Shinkafa’, rahotanni sun nuna cewa yana gudanar da yakin neman zaben cewa abokin hamayyarsa na siyasa, Sanata Kabiru Marafa bai lashe kujerar sanata a 2023 ba.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN