‘Yan bindiga sun kashe shugaban al’umma, dan kanensa tare da sace matan aure hudu a sabon harin Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani shugaban al’umma, Malam Ibrahim Abdullahi tare da kanensa a gidansu da ke kauyen Unguwar Mai Awo, a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna. Shafin isyaku.com ya samo.
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mata hudu, ciki har da wata uwa mai shayarwa a yayin harin da aka kai a unguwar da ke kusa da fitaccen garin Maraban Jos da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun far wa al’ummar ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 11 ga watan Junairu, 2023, inda suka yi ta harbe-harbe don firgita mutanen kauyen.
Wata majiya daga al’ummar yankin Abdullahi Auwal ta ce wasu mutanen biyu sun jikkata a harin inda daga bisani aka kai su wani asibiti da ba a bayyana ba domin kula da lafiyarsu.
“Sun kashe wani shugaban al’umma kuma shugaban kungiyar agajin gaggawa ta Fityanul Islam na yankin, Malam Ibrahim Abdullahi da dan uwansa Zakari Ya’u, ‘yan fashin sun kuma sace mata hudu ciki har da wata uwa mai shayarwa,” inji Auwal.
Daga ISYAKU.COM