Direbobin tanka sun tare hanyar Zaria zuwa Kano bisa zargin kashe abokin aikinsu da sojoji suka yi (Hotuna)

Direbobin tanka sun tare hanyar Zaria zuwa Kano bisa zargin kashe abokin aikinsu da sojoji suka yi


An samu tashin hankali a hanyar Zariya zuwa Kano yayin da direbobin tanka masu zanga-zanga suka tare hanyar da ke cike da cunkoson jama'a bisa zargin kashe abokin aikinsu da wani soja ya yi. Shafin isyaku.com ya samo.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a kusa da Tashar Yari a karamar hukumar Makarfi ta jihar Kaduna da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, 2023.

Kawo yanzu dai ba za a iya sanin ko me ya janyo cece-kuce tsakanin sojan da ke wani kamfanin gine-gine da marigayi direban motar ba.

Da yake tabbatar da toshe hanyar da direbobin masu zanga-zangar suka yi tare da kashe direban, mukaddashin kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Lawal Garba ya ce an tuntubi sauran jami’an tsaro da su taimaka wajen warware matsalar domin bude babbar hanyar ga masu ababen hawa.

“Tsayewar hanyar ta samo asali ne bayan da wani soja da ke aiki a kamfanin gine-ginen da ke aikin titin ya harbe direban tankar mai sakamakon rashin fahimtar juna, inda direbobin tankar suka rufe hanyar gaba daya domin nuna adawarsu,” in ji Garba.

“Na tuntubi Daraktan DSS, Kwamishinan ‘yan sanda da kuma NURTW, na kuma sanar da daraktan tsaron cikin gida na jihar halin da ake ciki, muna kokarin shawo kan lamarin,” in ji shi.

Kamar yadda Daily trust ta ruwaito, tuni wanda ake zargin yana hannun sojoji.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yekini Ayoku, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.



Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN