An gano gawar wata mata mai zaman kanta a dakin Otal a kan hanyar tsohuwar kasuwa a birnin Onitsha na jihar Anambra. Shafin labarai n isyaku.com ya ruwaito.
Majiyarmu ta ce matar yar asalin jihar Enugu ce kuma sunanta Chisom, ta mutu ne ranar Litinin 30 ga watan Janairu 2023 bayan ta gama wanke kwanonin abinci.
An tarar da gawarta rataye a dakin Otal. Sai dai har yanzu ba a san musabbabin mutuwarta ba.
Chisom tana zaune a dakin otal. Sai dai makwabta sun gudu bayan sun sami labarin mutuwarta.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI