Ku gaya wa 'yan siyasa su kawo 'ya'yansu ku je tare idan sun bukaci ku yi masu bangan siyasa - Tambuwal ga matasa
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bukaci matasa kada su yarda a yi amfani da su a zaman yan bangan siyasa a zaben 2023.
Tambuwal ya yi wadannan Kalaman ne yayin wani gangani na jam'iyar.ya gaya wa matasa cewa idan yan siyasa sun bukace su day su yi masu bangan siyasa, ya ce matasa su gaya aa yan siyasan cewa su je su yi amfani da yayan su marmakin su matasan.
Ya bukaci matasa kada su bari a yi amfani da su wajen haddasa rkici da tashin hnklai cikin al'umma.
Ya ce:
" Duk Dan siyasa da ya bukaci ku yi masa aikin bangan siyasa ku gaya masa cewa ya kawo yayans ku yi tare da su"