Mutum 20 sun mutu a Kebbi sakamakon hatsarin jirgin ruwa


Akalla manoman shinkafa 20 ake fargabar sun rasu sakamakon kifewar jirgin ruwa da dare a yankin Karamar Hukumar Koko/Besse da ke Jihar Kebbi. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Shugaban Karamar Hukumar Koko/Besse, Yahaya Bello, ya ce iftila’in ya auku ne a lokacin da jirgin ruwan ke dauke da manoma kimanin 100 a ranar Talata.

“Fasinjojom da lamarin ya shafa kusan baki dayansu matasa ne, maza da mata; Mun gano gawarwakin mutum 10, hudu mata da maza shida.

“Mun ceto kimanin mutum 80 kuma muna ci gaba da bincike domin gano sauran da suka bace,” in ji shi ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Laraba.

Ya ce hatsarin ya auku ne a lokacin da manoman shinkafan ke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Samanaji.

Shi ma dai kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar iftila’in.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN