Kwatsam maigida da matarsa sun mutu a Kano suna tsakiyar barci, an gano dalilin mutuwarsu

Kwatsam maigida da matarsa sun mutu a Kano suna tsakiyar barci, an gano dalilin mutuwarsu


Wani magidanci mai suna Sulaiman Idris, mai shekara 28 tare da matarsa Maimuna Halliru, mai shekara 20, sun mutu yayin da suke barci a gadonsu a cikin dakinsu a jihar Kano.  Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samo.

Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kano SP Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Laraba. Ya ce an gano gawakin ma'auratan ne ranar Litinin 2 ga watan Janairu 2023.

Ya ce lamarin ya faru ne a kauyen Kwa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa. Ya ce binciken farko ya nuna cewa ma'auratan sun mutu ne bayan sun rufe kofar daki kuma suka hasa wuta a gawayi domin dumama daki saboda sanyi.

Ya ce kakar marigayin ce ta banke kofa da safe kuma ta kula da tsananin hayaki a cikin dakin.

Yan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN