Maigida ya yi wa matarsa uwar yara 5 duka har lahira saboda burodi


Wata matar aure Mai suna Ogochukwu Anene, yar asalin kauyen Umuokpu a garin Awka na jihar Anambra ta mutu bayan mijinta mai suna Mr Ndubisi Wilson Uwadiegwu dan asalin jihar Enugu ya yi mata dukan ajali saboda burodi. Shafin isyaku.com ya samo.

Bayanai sun nuna cewa Rikici ya barke ne byan matar ta bukaci mijinta ya siyo burodi saboda kalacin yara. Sai dai mijin ya ce baya da kudi. Sakamakon haka matar ta je ta siyo burodi sanda daya da kudinta. Daga bisani mijin ya shiga dakin dafa abincin ya cinye burodin gaba daya.

Bisa wannan dalili matar ta tambayeshi dalilin da ya sa ya cinye burodin ba tare da ya rage wa yaransu ba. Nan ne mijin ya rufeta da duka har ta yanke jiki ta fadi kuma ta mutu bayan yan awanni.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN