Kuma dai: Gwamna Bagudu ya ki biyan bashin N110m da NBC ke bin jihar Kebbi na lasisin KBTV, KBRadio, ko za a rufe tashoshin?


Gwamnatin jihar Kebbi ta kasa biyan kudin sabunta lasisin gidajen Talabijin da na rediyon jihar da kudinsu ya kai fiye da N110m. Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo.

Tun ranar 11/11/2021 hukumar kula da gidajen watsa labarai ta kasa National broadcasting Corporation NBC, ta aike wa Gwamnatin jihar Kebbi takardar neman a biya kudaden.

Sakataren NBC, Igomu Onoja. Phd ne ya sa hannu a takardar wanda adadin kudin da NBC ke bin Gwamnatin jihar Kebbi sun kai Naira miliyan dari da goma, da dubu dari biyar  (N110.500.000.00).

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa an aika takardar zuwa ga Kwamishinan labarai da al'adu na jihar Kebbi, kuma aka kai takardar ga Gwamnatin jihar Kebbi.

Sai dai kawo yanzu bayani na cewa har zuwa lokacin rubuta wannan labari Gwamnatin jihar Kebbi bata biya wadannan kudaden ba.

Bisa dokokin hukumar NBC dai, za ta iya rufe gidajen Talabijin, rediyo ko kafar watsa labari da suka kasa biyan kudin haraji ko lasisin gudanarwa.

Lamari da ya sa ya ke da matukar muhimmanci Gwamnati ta biya NBC domin jama'ar jihar Kebbi su ci gaba da amfana da gidajen watsa labarai mallakin jiharsu, duba da cewa Gwamnatin Abubakar Atiku Bagudu za ta zo karshe cikin yan watanni masu zuwa.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN