Kano: Daga rabon fada, an sokawa matashi wuka a hannu, yanzu an yanke hannun baki daya


Matashi Salisu bai taba sanin sasanci da tsaida kwantar da tarzoma da shiga tsakanin makwabtansa 2 a Kano zaiyi sanadiyyar nakasarsa ba ta hanyar da bai yi tsammani ba. Legit.ng ya wallafa.

Lamarin wanda ya auku a yankin Fagge cikin garin Kano yayi sanadiyyar da Husaini, matashin mai shekaru ashirin da daya yayi rashin hannunsa sakamakon soka masa wuka da wani hatsabibi, Abubakar Ayuba, da ake kira da Namama a yankin yayi.

City & Crime sun tattaro yadda rikici ya barke tsakanin Namama da matashi Abdullahi Muhammad, wanda ake kira da Alhaji Ozil, a karshen watan Maris, wanda yayi tsanani yayin da Salisu ya ga ya dace ya shiga lamarin don kwantar da rikicin amma daga karshe aka soka masa wuka wanda yayi sanadiyyar shigar cutar tatanos.

Yayin labarta yadda lamarin ya auku a gadon asibitinsa inda aka cire masa hannun, Hussaini yayi kira da babbar murya ga hukumomi da su samar masa 'yancinsa saboda bai taba tunanin rasa hannunsa ba.

A cewersa:

"A yayin da na gansu suna fada tare da barazanar kashe junansu, nace bari in shiga tsakani yadda za a samu lumana.

"Na tunkari Namama tunda na san irin rigimarsa gami da shawartarsa da ya kiyayi barazanar halaka mutane. Amma sai ya zaro wuka yayi yunkurin caka min a cikina, yayin da na kauce, ya soka min a hannu.

"An kai ni asibiti inda suka bukaci mu zo da tare da 'dan sanda. Bayan an duba ciwon, hannuna bai warke ba.

"Sai muka tafi Asibitin Murtala Muhammad inda suka tura mu asibitin Malam Aminu AKTH daga baya zuwa nan Asibitin Kashi na Dala inda suka tabbatar da hannun ya lalace kuma dole a cire shi."

Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da aukuwar abun inda ta bayyana yadda suka kama wanda ya aikata mugun abun.

Ba a nan barawo ya tsaya da masa illa ba, ya sace sadakin da zai biya a daura auren yayin da aka je daurin auren.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN