Idanun ’yan siyasa sukan rufe da zarar sun samu mulki —Jonathan

Idanun ’yan siyasa sukan rufe da zarar sun samu mulki —Jonathan  


Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya hori ’yan siyasa da su rika bai wa bangaren shari’a damar gudanar da ayyukan da Kundin Tsarin Mulkin kasar ya tanada, yana mai cewa idanun ‘yan siyasa sukan rufe da zarar sun samu mulki. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Jonathan ya yi wannan nasihar ce a lokacin rufe liyafar karramawa da kuma kaddamar da littafi da aka kwashe tsawon mako guda ana yi wa Babbar Alkalin Jihar Bayelsa, Mai shari’a Kate Abiri da ta yi ritaya.

A taron da aka yi a Yenagoa, babban birnin jihar, Jonathan ya jaddada rawar da mai shari’a Abiri ta taka lokacin da ta rantsar da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda a cewarsa hakan ya dakile rikicin tsarin mulki a jihar.

Ya shawarci ‘yan siyasa a kan kada su rufe idanu saboda karfin da suke da shi, yayin da ya bukaci jami’an shari’a da su yi kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana da jajircewa wajen tabbatar da doka da oda, wanda ya ce yana da matukar muhimmanci wajen wanzuwar adalci.

Ya ce: “Ina shawartar ’yan siyasa cewa, a lokacin da muke ganiyar mulki, kada mu yi kokarin yi wa bangaren shari’a zagon kasa, saboda bangare ne da ya cancanci a kiyaye tsare-tsare da al’adunsa.

“Idan muka samu mulki a siyasance, sai mu runtse idanunmu. Saboda haka ya kamata ’yan siyasa su sani cewa al’umma tana lura da abin da ke faruwa.

“A yau, muna bikin babbar alkalinmu da ta yi ritaya saboda ta yi aiki da nagarta. A shekarar 2015, ta bar Bayelsa zuwa Ribas domin rantsar da gwamnan jihar wanda a dalilin hakan ya kawo karshen rashin zaman lafiya.

“Wannan shi yake nuna cewa bangaren shari’a ya fi na zartarwa nauye-nauye.”

A nasa jawabin, gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yaba wa mai shari’a Abiri bisa gagaruman nasarorin da ta samu, inda ya ce a tsawon shekaru 15 da ta yi a matsayin babbar alkali, ta rantsar da gwamnoni uku a Bayelsa da daya a Ribas.

Gwamnonin da mai shari’a Abiri ta rantsar sun hada da Cif Timipre Sylva a 2008 da Sanata Seriake Dickson a 2012 da Sanata Douye Diri a 2020 da kuma Nyesom Wike a 2015.

Gwamna Diri ya bayyana mai shari’a Abiri a matsayin wani tambari na shari’a, wadda ta yi aiki da nagarta a tsawon shekaru talatin a bangaren shari’a.

Ya ce duk da a yanzu ta yi ritaya, jihar ba za ta gushe ba wajen neman taimako da shawarwarinta saboda jajircewarta da kuma kwarewarta

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN