Hotuna: CP Kebbi ya karbi sabbin jami’an ‘yan sanda 262 daga PTS Sokoto, ya bukaci su sa kwarewa a yayin gudanar da ayyukansu

CP Kebbi ya karbi sabbin jami’an ‘yan sanda 262 daga PTS Sokoto, ya bukaci su sa kwarewa a yayin gudanar da ayyukansu


A ranar Talata 03/01/2023 Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, CP Ahmed Magaji Kontagora ya karbi tare da gabatar da jawabi ga sabbin ‘yan sanda 262 da suka kammala samun horo daga makarantar koyon aikin Yan sanda PTS, Sakkwato, aka aika su zuwa Jihar Kebbi, a hedikwatar rundunar a garin Birnin Kebbi.

Bayan taya su murna, CP ya umarce su da su kasance masu ladabi da ƙwarewa yayin gudanar da ayyukansu, ya bukace su da su kasance masu zaman kansu, masu ladabi da mutunta haƙƙin ɗan adam na mutanen da suke yi wa hidima, guje wa shaye-shaye yayin da suke bakin aiki, da guje wa barin wajen aiki har sai an canje su yadda ya kamata, tabbatar da bin  lokaci, kau da kai daga tafiyar dare, kaurace wa tafiye-tafiye sanye da tufafin aiki, da kuma kiyaye harkokin kafafen sada zumunta, musamman a lokutan zabe.
Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN