Da Duminsa: Mutum 3 Sun Jigata Yayin da Tagwayen Bam Suka Tashi a Kamfen din APC


A kalla mutane uku sun samu raunuka ranar Alhamis, yayin da wasu abubuwa masu fashewa suka tashi a zagayen kamfen din APC a filin wasan Rumuwoji cikin Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas. Legit.ng ta ruwaito.

Biyu daga cikin wadanda suka samu raunukan mata ne, inda duk aka garzaya da su asibiti don ceto rayuwarsu.

Sakataren watsa labarai na APC, Darlington Nwauju ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya siffanta hakan a "abun alhini,".

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Iringe-Koko ya ce zai bawa wakilin Punch cikakken bayanin kan lamarin.

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN