Atiku zai tashi a tutar babu a wata jihar da ya saka rai, jiga-jigan PDP sun bi Tinubu


Tsohon mamban majalisar wakilai ta kasa, Hon. Daniel Reyenieju ya bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC a jihar Delta. Legit.ng ya wallafa.

Reyenieju, wanda ya wakilci mazabar Warri a majalisar kasa har sau uku ya bayyana a hukumance cewa shi ba dan PDP bane daga ranar Litinin 16 ga watan Janairu, kana ya bayyana shiga APC.

Dalilin da yasa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

A cikin takardar barinsa PDP, tsohon dan majalisar ya bayyana cewa, ya bar PDP ne saboda rashin tabuka komai a jihar Delta.

Ya ce duba da wannan, ya ce ba zai ci gaba da zama a jam’iyyar ba, ya sauya sheka zuwa APC mai mulkin kasa.

A cewar rahoton Nigerian Tribune, Reyenieju ya yi addu’ar Allah ya dafa masa a harkokinsa na siyasa da ya kuma kawo dauki ga gwamnati a jihar Delta.

Legit.ng ta tattaro cewa, dan majalisar ya samu tarba daga jiga-jigan APC a jihar a wani gagarumin biki da aka yi.

Da yake magana a wurin taron, Reyenieju ya yi alkawarin tallata APC da tare da tabbatar da ta yi nasara a zabukan da ke tafe nan kusa.

Ya ce PDP ba gidan zai ci gaba da zama bane saboda mambobinta sun saba daga manufofin jam’iyyar, ya kuma ce ya shiga APC ne don kubutar da jihar Delta daga rugujewa.

Sauran wadanda suka bar PDP, suka koma APC

Baya ga Reyenieju, akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka bayyana ficewa daga jam’iyyar ta PDP tare da yin mubaya’a ga tsagin Tinubu, Naija News ta ruwaito.

Daga cikinsu akwai tsohon dan majalisar dokokin jihar, Hon. Tonye Timi da kuma tsohon hadimin gwamna Okowa, Kwamared Micheal Akpobire.

Dan takarar sanata na jam’iyyar APC a mazabar Delta ta Kudu, Hon. Joel-Onowakpo Thomas ne ya karbi sabbin mambobin.

Ya bayyana su a matsayin mutanen da ke kwarewa a siyasa da rayuwa, kuma za su kawo ci gaba a APC.

A irin wannan yanayin ne dan takarar shugaban kasa a NNPP, Kwankwaso ya rasa mambobin jam'iyyar sama da miliyan 2.8.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN