Da duminsa: Fusatattun matasa sun fasa allon da Buhari ya kaddamar da aiki a Katsina


A daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake tsaka da kaddamar da ayyuka a Jihar Katsina, wasu fusatattun matasa sun fasa allon da shugaban ya kaddamar da aiki. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Matasan dai wadanda da alama na nuna fushinsu ne da halin matsalar tsaro da ta canjin kudin da ake fama da ita a Jihar sun fasa allon bude gadar kasa Kofar Kaura da ke cikin Katsina.

Shugaba Buhari dai ya fara ziyarar aiki a Jihar ce wacce ita ce mahaifarsa a ranar Alhamis, inda ake sa ran zai bude wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Jihar ra aiwatar.

Daga cikin ayyukan dai akwai gadar kasa ta Kofar Kaura da wajen tara ruwa da ofishin tattara kudaden shiga da hukumar kula da yanayi da babbar asibitin cikin gari na Katsina.

Kazalika, Buhari zai kuma kaddamar da kamfanin casar shinkafa wadda hamshakin dan kasuwar nan. Alhaji Dahiru Mangal, ya gina.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN