Da dumi-dumi: Babban mai kula da harkokin dalibai a wata jami'ar kudu ya kone kurmus a hatsarin mota


Babban jami’in kula da harkokin dalibai na jami’ar Neja Delta ta jihar Bayelsa, NDU, Dokta Ayasen Kemeakigha, ya kone kurmus a wani hatsarin mota da ya afku a kan babbar titin Tombia Amasomma a lokacin da yake kan hanyarsa daga makarantar zuwa Yenagoa.  babban birnin jihar a ranar Asabar, 21 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya fitar, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mamacin shi kadai ne ke cikin motar.

“A ranar 21 ga watan Janairun 2023 da misalin karfe 14:45 ‘yan sanda suka mayar da martani ga wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan titin Tombia-Amassoma a jihar Bayelsa, inda suka gano cewa mutum daya tilo a cikin motar, Toyota Corrolla tare da Reg.  N0.  06H 132 BY ya kone kurmus.

Da aka gudanar da bincike, an bayyana cewa marigayin shi ne Dokta Ayasen Kemeakegha, mai shekaru 55, shugaban kula da harkokin dalibai na jami’ar Neja Delta, Amassoma. Tuni dai aka kwashe gawar zuwa dakin ajiyar gawa.  Ana ci gaba da bincike.”

Har yanzu cibiyar ba ta ce uffan ba kan wannan lamari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN