Matasa 2 sun mutu a cikin masai bayan sun shiga domin aikin yaso a Kano


Maza biyu, dan shekara 17 da dan shekara 27, sun mutu a cikin wani masai da ke Kasuwar Sabon Gari da ke karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano a ranar Asabar da ta gabata yayin da suke aikin yashe masan. 

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana a Kano ranar Lahadi cewa hatsarin ya faru ne da dare.

Ya bayyana cewa matashin mai shekaru 27 a duniya yana aiki ne a cikin magudanar ruwa lokacin da ya makale kuma a kokarin ceto shi abokin aikinsa, matashin mai shekaru 17 ya shiga cikin babban rami mai fadi kuma shi ma ya makale.

"Mun sami kiran gaggawa game da hatsarin kuma nan da nan muka aika da tawagar ceto zuwa wurin," in ji shi.

Ya kara da cewa hukumar kashe gobara ta fitar da mutanen a sume sannan suka kai su asibitin Murtala Muhammad na musamman inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwarsu.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa an mika gawarwakin ga ’yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda na Sabon Gari.

Ya danganta mutuwar mutanen da yawan zafin jiki da rashin iskar oxygen a cikin ramin bayan gida.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN