Bayan kin amincewa da bukatar shugaba Buhari, gwamnan PDP mai karfi a jihar arewa ya yi zargi mai illatawa ga APC
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta tsorata wajen nuna ayyukan more rayuwa da gwamnatin sa ta gudanar ga maziyartan. Legit.ng ya ruwaito.
Gwamnan ya ce wannan ne dalilin da ya sa ‘yan adawa a jihar suka yanke shawarar kaddamar da yakin neman zabensu na gwamna a jihar daga wajen Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Fintiri, wanda ke neman wa’adi na biyu a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a baya an ruwaito cewa ya ki amincewa da bukatar APC ta yin amfani da dandalin Ribadu a babban birnin jihar.