An tsinci gawar wata mata a birnin Minna (Hotuna)


An tsinci gawar wata mata da ba a san ko wacece ba a jibge a Farm center a Minna, babban birnin jihar Neja. 

Wani ganau, mai suna Comr Lanre Sadiq, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a kafar sada zumunta, ya ce an gano gawar ne a daren ranar Asabar, 7 ga watan Janairu, 2023.

A cewarsa, mazauna wani unguwar sun yi ikirarin cewa a ranar ne aka ga wani mai suna Baba Muhammed ya kai wata mata cikin dakinsa. Daga bisani aka ga yana hidimar kokarin jibge gawarta.

Lamari da ya sa jana'a suka kira yan sandan Tudun wada kuma suka kai gawar babbar Asibiti domin ajiye gawar.

Wacce aka sami gawarta bata da wata alamar shaida, kuma bata da wayar salula balle a nemo ahalinta.


Daga ISYAKU.COM

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN