2023: "Tsunami za ta afkawa APC" Tsohon gwamna ya ce zai kawo karshen mulkin jam'iyya mai mulki a jihar Arewa.

2023: "Tsunami za ta afkawa APC" Tsohon gwamna ya ce zai kawo karshen mulkin jam'iyya mai mulki a jihar Arewa.


Tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Ahmad Mahmud ya bayyana rashin gamsuwa da ayyukan jam’iyya mai mulki a jihar. Legit.ng ya wallafa.

Mahmud wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP a wani gagarumin yunkuri, ya sha alwashin kawo karshen tafiyar da mulkin jam’iyya mai mulki a jihar, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Tsohon gwamnan ya mayar da martani, ya kuma yi kakkausan alwashi ga APC

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani ga kalaman gwamna Mohammed Badaru na baya-bayan nan yayin wani gangamin siyasa, cewa ba abin dogaro ba ne, kuma ya ce jam’iyyar APC za ta tura jam’iyyar PDP mai adawa zuwa kabarinta a shekarar 2023.

A cewar Mahmud.

“Ina so in tabbatar muku da cewa tsunami zai afkawa jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa, “Tuni na tuntubi abokan siyasa na da sauran mutanen jihar Jigawa a APC, duk sun amince su fice daga jam’iyyar zuwa PDP domin ceton masoyanmu da jihar mu."

Mahmoud ya koka a yayin da ya sha alwashin kawo karshen mulkin APC a jihar Jigawa, ya yi alkawarin marawa PDP baya

Sai dai ya yi alkawarin hada hannu da sauran ‘yan jam’iyyar PDP da kuma mutanen jihar don tabbatar da cewa jam’iyyar (PDP) ta dawo kan karagar mulki a 2023.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN