Zaben 2023: Matar Atiku ta dau kamfen zuwa wani matsayi, ta ba mutane da yawa mamaki a babban jihar Arewa


Jihar Bauchi - Rukayya Atiku Abubakar, matar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, a ranar 6 ga watan Disamba, ta dira jihar Bauchi don yin kamfen gabanin babban zaben 2023. Rahotun legit Nigeria.

Ta isa Bauchi don neman mata su goyi bayan mijinta tare da mambobin kungiyar ta na Princess Rukaiya Atiku Campaign Organisation (PRACO), rahoton Pulse.ng.

Ziyarar da Rukaiya ta kai jihar Bauchi na zuwa ne bayan kamfen da wasu ayyuka da ta fara tun fara yakin neman zabe.

A baya-bayan, Rukaiya ta shirya tarukan jin ra'ayin mutane a yankunan arewa da dama don tattauna hanyoyin karfafa rawar da mata za su rika takawa a dimokradiyya.

Tana kuma kan gaba wurin ilmantar da mata a karkara kan shirin farfado da kasa na Atiku da samar da mafita ga dimbin matsalolin da suka shafi cigaban mata idan an zabe shi shugaban kasa a 2023, Daily Post ta rahoto.

Kuma, a wani hira Rukaiya ta ce:

"Mijina, Atiku Abubakar, shine kadai dan takarar shugaban kasa a zaben da ke tafe a 2023 da ke goyon bayan damawa da mata da matasa a gwamnati. Don haka ne ya yi alkawarin ware $10 biliyan don karfafawa matasa da mata."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN