Yadda barawo ya sace waya kuma yayi ƙoƙarin tserewa daga shagon amma kofa ta ƙi buɗe (bidiyo)


Wani barawo da ya yi yunkurin satar waya a wani shago bai yi nasara ba lokacin da ya kasa bude kofar ya tsere da wayar. Shafin isyaku.com ya samo.

Mai shagon Afzal Adam, mai shekaru 52, ya yi amfani da gizmo da aka sanya a bayan kanti don kulle kofar shiga bayan ya shak'u da manufar barawon.

A cikin wani faifan bidiyo da aka raba ta yanar gizo, an ga barawon a wurin kantuna, yana nuna sha'awar wayoyin da ake sayarwa.

Daga karshe ya samu wayar da yake so, ya juyo da gudu ya nufi kofar.

Sai ƙofar ta ki buɗewa.

Ganin babu wata hanyar tsira yasa ya mayar da wayar kafin mai shagon ya bude kofar ya barshi ya fita.

Mai shagon a Kasuwar Waya da ke Dewsbury, West Yorks, Ingila, ya ce ya bar barawon ya tafi saboda yana fargabar zai iya yin tashin hankali. 

Latsa kasa ka kalli bidiyo

https://m.facebook.com/watch/?v=2105955032915932&paipv=0&eav=AfbgT92AAETbHbU-vDIT6pLTRoMuGw0uREOleMEv8p0SS4I5k41kfW6GavasQjDe-PA&_rdr

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN