Yanzu yanzu: Mumumar hadarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane da yawa, mata da yara a wata jihar Arewa


Wani bala’i ya afku a ranar Lahadin yayin da mutane shida suka mutu a wani hatsarin mota a kauyen Sabuwar Miya da ke karamar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi. Kampanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito
.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin rahoton zirga-zirgar ababen hawa da aka rabawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Bauchi ranar Lahadi.

Shugaban na FRSC ya kara da cewa wasu mutane 16 sun jikkata a hadarin.

Ya ce hatsarin daya tilo da ya rutsa da motar bas Toyota Hiace mai lamba BA124 AO6, ya faru ne da misalin karfe 11:50 na safe.

A cewarsa, sai da jami’an hukumar suka kwashe mintuna 20 kafin su isa wurin da hadarin ya afku domin share wurin.

Kwamandan sashin ya alakanta musabbabin faduwar motar da fashewar tayoyin mota da kuma rashin kulawa.

“Mutane 22 ne suka mutu a hadarin mota kuma akwai manya maza biyu, maza hudu, manya 10 mata da yara mata shida.

“Shida daga cikinsu sun rasa rayukansu a nan take kuma akwai manya mata biyu, yara maza biyu da mata biyu.

Abdullahi ya kuma bayyana cewa duka wadanda suka jikkata da sauran wadanda suka mutu an kai su babban asibitin Kafin Madaki domin samun kulawa da kuma tabbatar da su.

Ya kara da cewa an shirya kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH) don ci gaba da kula da su.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN