Tinubu, Atiku, Obi? A karshe babban Malamin adduni ya bayyana hasashen wanda ya lashe zaben 2023, ya ba da sharudda masu karfi


Kasa da kwanaki 70 kafin gudanar da zaben shugaban kasa na 2023, Babban mai kula da Ikilisiyar Ikklesiyoyin bishara ta INRI, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana hasashensa gabanin babban zaben. Legit.ng ta wallafa.

A cikin wata takarda da aka fitar a ranar Asabar, 24 ga Disamba kuma aka bai wa Legit.ng, Primate Ayodele, ya ce abin da ba a zata ba zai faru a shekarar 2023 a fagen siyasa.

Ayodele, wanda ya yi ikirarin cewa ba shi da wani dan takara a cikin wadanda za su fafata a zaben, ya ce Allah ya bayyana masa wasu sakonnin da suka shafi duk manyan ‘yan takara a zaben.

Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar  da kuma dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi sune manyan ‘yan takara a zaben.

A cewar Ayodele, Allah ya bayyana masa cewa idan Atiku ya ci zaben shugaban kasa, tattalin arzikin Najeriya zai inganta, ya kara da cewa idan Tinubu ya samu tikitin, Najeriya za ta dan samu sauki.

Ya bayyana cewa idan jam’iyyar Labour ta lashe zaben shugaban kasa, za ta zama gwamnati ga talakawa inda masu hannu da shuni ke korafi.

Primate Ayodele ya ce:

“Allah ya bayyana mani cewa idan Atiku ya ci shugaban kasa tattalin arzikin Najeriya zai inganta kuma idan dan takarar jam’iyyar APC, Tinubu ya samu tikitin, Nijeriya za ta dan samu sauki, idan jam’iyyar Labour ta lashe shugaban kasa za ta zama gwamnati.  ga talaka inda mai kudi zai yi ta gunaguni.

“Gwamnatin PDP za ta kasance ta talakawa da masu hannu da shuni, jiga-jigai a karkashin gwamnatin APC amma ’yan kasa za su ji dadin ta har da marasa ilimi.

A halin da ake ciki, Legit.ng  a baya  ta rahoto cewa wani Malamin addini na baya-bayan nan ya bayyana Peter Obi, Atiku Abubakar, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wa zai lashe zaben shugaban kasa a 2023.

An ruwaito cewa a cewar wanda ya kafa kungiyar One Love Family, Satguru Maharaj ji, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Tinubu, ya fi samun damar lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.

A yayin bikin cikarsa shekaru 75 a ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, Maharaj ji ya ce Tinubu zai kayar da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku, da kuma Obi na jam'iyyar Labour.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN