Yan bindiga sun kutsa Masallacin Juma'a sun yi awon gaba da Masallata a jihar Delta


Yan bindiga sun kutsa wani Masallacin Juma’a tare da yin awon gaba da kimanin mutum uku a ranar Juma’a a Jihar Delta. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN

) cewa maharan sun jikkata akalla mutum 11 a harin da suka kai a lokacin da ake tsaka da Sallar Asuba a Babban Masallacin Juma’a da ke garin Ughelli.

Wani ganau kuma makwabcin masallacin, mai suna Larry, ya ce karar harbe-harben maharan ne ya tashe su, “ana tsaka da haka kuma muka rika jin  kururuwar mutanen dake cikin Masallaciin suna neman agajin.”

Kakakin ’yan sandan jihar Bright Edafe ya tabbatar da harin, amma ya ce mutum 11 ne aka jikkata.

Kakakin, wanda bai ce komai game da batun garkuwa da mutane a masallacin ba, ya ce, “’yan sanda sun fara gudanar da bincike domin kamo maharan kuma nan gaba za mu sanar da ku.

“Amma kawo yanzu babu wanda ka kama kan lamarin, amma ina tabbatar muku cewa masu laifin za su shiga hannu,” kamar yadda ya shaida wa NAN.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN