‘Yan bindiga sun kashe mutum 7, sun yi garkuwa da 5 a wani sabon harin da aka kai a Sokoto

‘Yan bindiga sun kashe mutum 7, sun yi garkuwa da 5 a wani sabon harin da aka kai a Sokoto

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu biyar a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni a jihar Sokoto. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Al’ummomin da aka kai harin sun hada da Bare, Kagara, Kojiyo a karamar hukumar Goronyo da kauyen Faji a karamar hukumar Sabon Birni.

An bayar da rahoton cewa an kashe mutane shida a Bare da daya a Kagara.  An kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki daban-daban.

Shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, wanda ya tabbatar da harin, ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu dabbobi a kauyukan.

A cewar Goronyo, hare-haren sun faru ne da misalin karfe 4 na yammacin Laraba, 30 ga Nuwamba, 2022.

A kauyen Faji, an ce barayin sun yi garkuwa da mutane biyar da suka hada da mutum daya da matansa biyu.

Wadanda aka sace su ne Alhaji Yusuf, Suwaiba Isa, Dagumi da matansa guda biyu.

An yi jana’izar wadanda aka kashe a ranar Alhamis 1 ga Disamba, 2022.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN