Yadda jiragen yakin sojin Najeriya suka kashe ’yan ta'adda 100 rana guda a jihar arewa
Jiragen Yakin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram da kwamandojinsu sama da 100 a rana guda a Jihar Borno. Jaridar Aminiya ta wallafa.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ce jiragen yakinta sun yi raga-raga da ’yan Boko Haram din ne a yayin da suke tsaka da shirin aiwatar da wani hari a yankin Mantari da ke Karamar Bama ta jihar a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, 2022.
Kakakin rundunar, Edward Gabwek, ya ce, “An ba jiragen yakin umarnin yin luguden wuta tare da hallaka ’yan ta’addan ne” bayan samun bayanan sirri cewa sun shirya kai hari tare da wani jagoransu mai suna Ikirima, wanda ya dawo yankin Mantari da motocin yaki da makamai.
Edward Gabkwet ya ce “Bayan harin sama na farko, mayakan da suka tsallake rijiya da baya sun koma wurin domin daukar gawarwakin ’yan uwansu da jiragen yakin suka kashe, wanda hakan ya kara ba wa a jiragen damar aika sama da mutum 100 a cikinsu lahira, wasu gommai kuma suka samu munanan raunuka.”
Ya ce kwamdojojin ’yan ta’addan da aka kashe a hare-haren saman sun hada da Khalid Tukur, Maimusari, da kuma Bakura Jega.
Ya ce ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun shirya kai munanan hare-hare a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara da kuma Babban Zaben 2023, amma bayanan sirri da aka samu da wuri sun taimaka wajen dakile su.
“Samun bayanan shirinsu na kai hari a yankin Bama ya sa aka tura jiragen saman soji suka tarwatsa su tare da hana su damar taruwa ballantana su iya kai hari,” in ji shi.
Ya ce hare-haren da rundunar ta kai a baya-bayan nan sun gurgunta harkokin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.