Don guje wa matsaloli, duba wajen da Buhari zai koma bayan kammala mulkinsa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai koma Daura da zarar ya kammala wa’adin mulkisa don guje wa matsaloli. Rahotun Jaridar Aminiya.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Lahadi lokacin da ya karbi bakuncin mazauna Babban Birnin Tarayya don taya su murnar bikin Kirsimeti.
Kazalika, Buhari ya gode wa ’yan Najeriya da suka yarda tare da amince masa ya shugabance su.
Ya ce duk da ci gaba da aka samu a fasaha da kimiyya, hankalinsa zai fi kwanciya idan ya koma garinsa.
Buhari dai ya jima da cewa da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa zai bar Abuja gaba daya, don kauce wa shiga sabgogin gwamnatin da za ta gaje shi.