Jihar Kano - Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya ce ba gaskiya bane labarin da ake cewa gwamna Ganduje ya kore shi daga mukamin kwamishinan addinai na jihar Kano. Legit.ng ya wallafa.
Baba Impossible ya ce, shi ya yi radin kansa ya ajiye aikinsa sabanin zaton cewa an kore shi.
Ya bayyana wannan batu ne a wata tattaunawa da ya yi wa BBC Hausa, inda yace ya ba da takardar ajiye aikinsa tun a ranar 30 ga watan Disamba.
A cewarsa, tuni an karbi takardar, aka buga mata hatimi tare da ba shi kwafin takardar don ajiye a gaba, ya kuma bayyana cewa, bai fadi dalilin ajiye aikinsa.
Ganduje ne ya kori Baba Impossible
A bangare guda, wata sanarwa da kwamishinan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar ta ce, gwamna ganduje ne ya bayyana korar Baba Impossible.
Hakazalika, sanarwar ta ce, Dr. Nazifi Bichi ne aka bayar don maye gurbin Baba Impossible.
A cewar sanarwar, an kori Baba Impossible ne saboda rashin da’a a ka’idan aikinsa da kuma saba tsarin aikin gwamnati.
Hakazalika, kwamishinan ya ce ana zargin Baba Impossible da rashin yiwa gwamnati rashin biyayya.