Madalla: Buhari ya cika shekara 80 a Duniya

Buhari ya cika shekara 80 a Duniya


A ranar Asabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika shekara 80 a duniya. Jaridar Aminiya ta wallafa.

Buhari wanda aka haifa a ranar 17 ga watan Disamba, 1942 ya cika shekara 80 a duniya ne kwana 70 daidai kafin zaben wanda zai gaje shi a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

163 ke nan kafin saukarsa daga mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin shugaban kasa na 15.

Takaitaccen tarihin Buhari

Tun yana shekara uku Allah Ya yi wa mahaifinsa rasuwa, daga baya ya shiga aikin soji, inda ya halarci Yakin Basan Najeriya, kuma har ya kai matsayin Janar.

A lokacin da yake soja, ya zmaa shugaban kasa bayan juyin mulkin 1983, inda shi ma aka hambarar da gwamnainsa a 1985.

A matsayinsa na soja a yi ministan man fetur da Gwamnan Jihar Arewa maso Gabas wadda yanzu ta koma jihohi shida, baya ga wasu mukaman shugabanci da ya ya rike a zamanin mulkin sojan.

A zamanin mulkin soja na marigayi Sani Abacha, Buhari ya kasance shugaban hukumar PTF mai kula da asusun mai, matsayin da ya ja masa farin jini.

Shigarsa Buhari siyasa

Bayan dowawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a Jamhuriya ta hudu a 1999, sai a 2003 ya fara neman kujerar shugaban kasa a Jam’iyyar ANPP, amma ya sha kaye a hannun shugaba mai ci na lokacin, Olusegun Obasanjo.

A 2007 ya sake nema, amma ya sha kaye a hannun Umaru Musa Yar’Adua na Jam’iyyar PDP mai mulki.

A 2009 ya kafa Jam’iyyar CPC, wadda a karkashinta ya tsaya takara a zaben 2011, amma shugaba mai ci na wancan lokaci, Goodluck Jonathan na PDP ya kayar da shi.

Alkawuransa ga ’yan Najeriya

A shekarar 2013 jam’iyyun ACN, ANPP, da wani bangare na APGA da Sabuwar PDP suka hadu suka kafa APC, wadda a 2015 Buhari ya ci zaben shugaban kasa a karkashin inuwarta.

Shugaban Kasan da jam’iyyarsa sun yi wa ’yan Najeriya alkawarin samar da tsaro, farfado da tattalin arziki, yaki da cin hanci da rasha, farfado da noma, samar da ababen more rayuwa da sauransu

Gwamnatin Buhari

Sai dai gwamnatin tasa ta samu cikas, musamman wajen cika alkawuran bangaren tsaro da tattalin arziki.

Duk da cewa ayyukan Boko Haram da gwamnatinsa ta gada sun yi sauki matuka, matsalar ’yan bindiga ta kunno kai kuma har yanzu tana ci wa kasar tuwo a kwawrya.

Matsalar tsaro

’Yan bindiga sun sace dubban mutane, tare da raba wasu da garuruwansu, baya ga kona gidaje da yi wa mata fyade tare da karbar makudan kudade a matsayin fansa.

Kazalika ayyukan bata-garin ya hana-manoma zuwa gonaki, tare da sanya matafiya cikin fargaba, baya ga asarar rayukan jami’an tsaro.

A baya-bayan nan dai ’yan bindiga sun sace mutum sama da 60 a jirgin kasan Kaduna-Abuja, suka kashe wasu 10 a harin bom da suka kai wa jirgin; Sai bayan watanni suka saki ragowar fasinjojin da ke hannunsu.

Baya ga haka, sun sace tarin mutane kama daga sarakuna, ’yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, dalibai a makarnatun Islamiyya, firamare da sakandare da manyan makarantu da kauyuka, da matafiya a sassa daban-daban.

A yayin da matsalar take ci wa yankin Arewa tuwo a kwarya, kungiyar ta’ddanci ta IPOB mai neman ballewa daga Najeriya ta tsananta kai hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati, tare da sa wa mutanen yankin zaman gida dole a yankin Kudu maso Gabas.

Bayan kona cibiyoyin ’yan sanda, a baya-bayan nan, hukumar INEC ta ce an kai wa cibiyoyinta hare-hare 53, wadanda yawancinsu a yankin Kudu maso Gabas ne da ayyukan IPOB suka fi tsanani musamman a Jihar Imo.

Tattalin arziki

A bangaren tattalin arziki kuma, ’yan kasar na kokawa kan tsadar rayuwa, inda a watannin baya suka yi ta maganganu kan karin farashin lantarki da na man fetur, duk da cewa gwamnati ta janye hannunta a bangarorin.

A halin yanzu matsalar karancin man fetur, wadda tun hawan Buhari aka samu saukinta, ta dawo, musamman a shekarar 2022.

A  halin yanzu farashin mai kan kai Naira 200 ko fiye da haka a gidajen mai, a yayin da masu sayarwa ta bayan fage kan sayar da lita har a sama da Naira 400.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN